💦 *Talented writers forum* 💦
*had'in kanmu abin alfaharinmu🤝kungiya d'aya tamkar da dubu*
_domin samun littattafan mu shiga....
_To get access to talented novels check_
http://talentedwrittersnovel.blogspot.com/
💞💞 *Zumunci*💞💞
Na _*Sunhera*_
*dedicated to* _*Reefat yahya*_
❤❤❤ *my Faty Afreen ina tayaki murnar kammala littafin Ki _Mijin yarinya_ hakika labarin ya kayatar ya fad'akar up up Allah ya kara basira muna biye dake*😘😘😘
❤ _Happy anniversary islah tee ( Mrs jameel) Allah ya barku tare ya kara dankon love ameen_😘😘 ❤
_ina mika sakon taaziya ta gareki 'yar uwa @ ( y'ar aljanna) Allah ya jikan mamaci ya kai haske kabarinsa ameen , mu kuma Allah yasa mu cika da imani_
*fans kuyi hakuri da wannan am busy ne shiyasa kuka ji shiru nagode da zumunci😁🤝🏻 love u all*
*45&46*
Tunda safe ake gyara jikin Afreen har bayan azahar sannan aka sake cancara mata sabon zanen lalle tunda wancan ya goge ga kitso ma pherteenjay ta watsa mata mai shegen kyau kananu sosai sadey smart kuwa ta zama mata lalle me ratsin Ja da baki masha Allah Afreen tayi kyau sosai, Ruky kuwa sun share awa guda a waya tana mata huduba😂😂 su Ruky manja .matan Gidan gyara da talented fans group da zallar yaudara group Duk tsokanarta suke mum abla na cewa yau zaki ji maza😂😜 su anty dahare da Fatima maison mijinta kuwa ana private ana watsa nasiha na kissa da kisisina yanda xaa xauna da Salina a yayinda Rabia da Ruhaimah suke mata waazi akan ladadi da biyayya. Ummu waleed da Sadee Adam kuwa ana lectures akan girki sai su anty maryam Lawal da Reefat tawa kuma ana bada points akan love😜 Afreen dai masha Allah kota ina ta karu gaskiya taji dadin haduwa da wannan bayin Allah, su Ummee kuwa uwar tsoka tare da Rafiat zaizam sai tsokar Afreen suke wai ynxu kam an saduda ne? Ta mika wuya kenan.. (Lol love u all @ readers)
*8:20pm* Shuraim ya kira phn nata ya shaida mata yana kofar gida ta fito su tafi..hhh kaji maza, Afreen kam kwanciyar ta tayi tana ganin rashin kunya ne idan tace da mami yana jiranta a kofar gida. Ya share muntuna 20 yana zaman jira ganin shirun yayi yawa ne yasa dole ya fito ya shiga gidan dayake babu jama'a kai tsaye falon Abba ya wuce yana nan yana kallon news sallama yayi ya shiga ya xauna, cikin girmamawa suka gaisa yayi shiru kansa na kallon kasa donhaka Abba ya cire waya ya kira mami ya shaida mata Shuraim ya zo cikin kankanin lokaci mami ta shigo tare da Afreen nan Abba ya musu nasiha godiya sukayi Afreen kam ido ya raina fata lallai yau xata shiga sabon rayuwa xata rabu da iyayenta nan ta fara kuka dakyar mami tayi karfin hali ta hau rarrashi daga karshe sukayi sallama tabi bayan mijinta suka tafi.
Tafiya suke babu Wanda yayi magana cikin su har suka karasa gidan nan ya fito tana xaune har ynxu kuka take, batayi aune ba taji ya bude murfin bangaren da take cak! Ya d'aga ta Xuwa part nata bai sauketa ko'ina ba sai kan gado sannan yayi ficewarsa, a hankalin ta bude ido tana bin d'akin da kallo tsarin ya mata kyau batasan lokacin da murmushi ya kubce mata bah tace " wow ..gaskiya d'akin yayi tanx mami tanx Abba na nagode muku Allah ya saka*" Reefat tace ohh..sunhera kina jin yaran zamani babu ko kunya, mu lokacin mu guduwa mukayi aka nememu aka rasa..lols , bayan 30 mins bata ji motsin komai ba dayake dama tayi wanka tun a gidan su donhaka kai tsaye wardrobe ta nufa ta bude an shirya mata komai yanda ya kamata nan ta xare kayan bacci rigace da doguwar wando pink color ta cire kayan jikinta ta sanya su sannan ta wuce gaban dressing mirror ta fesa turaruka masu qamshin gaske sannan ta fesa hair spray da wani mint me qamshin strawberry daga nan ta kwanta tare da tofa adu'oi.
Shuraim ya shigo tare da sallama ganinta yayi xaune ta buga tagumi daga ganinsa Kasan yana cikin farin ciki, gefenta ya xauna " mum Khalid yadai" harara ta galla masa tare da kawar da fuska gefe. Hannu yasa ya jawota jikinsa kamar jira take ta fashe masa da kuka tana cewa " shikenan burinsu ya cika sun rabani da kai Allah ya isa"
"Su waye kenan?" Ya tambaya cikin jin haushin kalaman nata , kai tsaye tace " munafukan da suka had'a auren mana shegu azz..." Bata karasa ba ya ajiye mata lafiyayyen mari ya nuna ta da yatsa yace
"Kul! Ki zagar min iyaye wllhi ranki sai ya mugun baci shashasha kawai Mara hankali" yana gama fadar haka ya tashi fuu ya fice .kuka take tana zage zage kamar mahaukaciya sai kuma gashi ya shigo fuskar nan a murtuke ya ajiye mata wata bakar Leda sannan ya fice. tuni qamshin kazar ya gauraye d'akin sai da 'yawun smart ya tsinke Reefat tace ke dai kinyi asara da wannan kwadayin naki lol sunhera tace kuzo mu bi bayan ango mu gano gulma a can bangaren amarya , aikuwa babu b'ata lokaci muka garzaya bangaren Afreen Ku biyomu.😘
Cikin bacci taji ana Jan yatsun kafarta a hankali ta bude ido ganinsa tayi cikin kayan bacci sai qamshi ke tashi murmushi ya sakar mata mai sace xuci ta lumshe idanunta " baby na tashi Ki ci abinci " cikin murya me daukar hankali tace " na k'oshi yaya bacci zanyi"
A hankali ya jawota ta dawo jikinsa yana shafa mata baya tamkar mai rad'a yace " pls baby bana son Ki kwana da 'yunwa"
Marairaice masa tayi tare da cewa " Allah bacci nake ji" "is OK let's sleep" daga nan ya gyara mata kwanciya ya kulle kofar tare da kashe wuta sai bedside lamp kadai ya bari sannan ya haye gadon zuciyar Afreen na dukan 3-3 sai ji tayi yana karanta aduoin bacci sannan ta sauke numfashi, adua yayi ya kwanta tare da jawota jikinsa ya matseta gam rad'a ya mata a kunne yace " gud nyt my baby kiyi mafarki dani I love u " peck ya manna mata a kumatu murmushi Afreen tayi ta lumshe ido tace " u too" daga nan suka rungume juna tare da yin bacci cikin kwanciyar hankali.
Washegari Shuraim ya tashesu sallar asuba sannan ya wuce masallaci Afreen tana idar da salla ta bude Qur'an tana karantawa, karfe shida da rabi tayi adua ta rufe daga nan ta wuce kitchen kasancewar Shuraim bai shigo ba yana can bangaren Salina. Ta duba store nata akwai kayan abinci nan ta feraye dankalin turawa mai dan yawa ta kunna gas nan ta dora mai a wuta sannan ta yanka shi a tsaitsaye ta fara soya shi, cikin kankanin lokaci ta gama daga nan kuma ta soya kwai daban ta xuba a cikin warmer sannan ta tafasa ruwan zafi da Lipton hade da kanunfari da citta ta juye a flask, dama indomienta na kan wuta bayan ya tafasa ta cakuda shi cikin kwai Wanda ta sa kayan hadi irinsu magi albasa da sauransu a ciki. Mai ta xuba a frying pan tayi frying nashi ya nuna yanda take so ta sauke ta juye a food flask daga nan ta kashe gas d'in.
Dining table ta shirya komai sannan ta wuce d'akin ta wanka tayi ta fito ta tsara kwalliya cikin atamfa mai shegen kyau dinkin touch me ne na riga da siket me matukar daukar hankali ta feshe jikinta da kalolin turaruka masu qamshi hade da humra dinta , daga nan ta gyara gado ta kunna burner ta xuba turaren wuta a ciki sannan ta fesa room fresh tare da kunna A.c ta kashe fan kuma ta sauke labule nan d'akin yayi duhu Kadan ga kuma mugun qamshin dake tashi hmmmm...so romantic 'yar uwa sai kin gwada. A can falo ma haka ta gyara ko'ina sai qamshi kake ji sai da ta gama sannan ta wuce toilet nan ma ta gyara komai tsab ta fito kenan tana duba agogo karfe takwas da rabi 8:30 dai-dai nan Shuraim ya shigo cikin shirinsa na Xuwa aiki shadda milk color ne a jikinsa yayi kyau sosai " ina kwana yaya"
Murmushi yayi ya jawota yana cewa " bafa haka ake yi bah ,OK lemmi teach u ( bari na koya miki)" peck ya manna mata a goshi tare da cewa " I miss u " ya sake yin wani a kumatu yace " I need u" sannan ya hada bakinsa da nata yace " I love u! dafatan kin tashi lafiya " gaba daya jikin Afreen ya mutu murmushi take a yayinda kanta ke kallon kasa , hannu ya saka ya d'aga habarta tare da girgiza mata kai " babu kunya tsakanina dake ni Mijin Ki halalinki ne donhaka Ki daina jin kunya ta , Ki sake jiki Ki nunamin so da kulawa pls" a hankali tace " yaya muje kayi breakfast kada ka makara " babu gardama ya rike hannunta suka wuce falo kai tsaye dining area suka nufa ta xuxxuba masa komai sannan ta had'a masa tea mai kauri Wanda qamshi ya cika shi, bismilla ta masa bayan ta xuba nata kad'an nan suka fara ci ko kuma ince Shuraim na ci domin ita Afreen kunya ya hanata sakewa sai juya spoon take ya lura bata ci amma baiyi magana a cikin zuciyar sa cewa yayi " yarinya zaki ma daina " haka suka cigaba da zama Shuraim ya cinye Wanda ta xuba mishi tas ya dora tea a kai sai da ya gama yayi hamdala sannan ya kalleta yace " nagode my baby Allah ya miki albarka " "Ameen " ta amsa cikin jin dad'i daga nan ya tashi yace " ni zan wuce ina da class by 10 so Ki kula da kanki " " Allah ya tsare ya bada sa'a" "Ameen nagode " har ya juya zai tafi sai kuma ya dawo kusa da ita yayi kasa kasa da murya yace
" ko yar kiss din nan babu bare rakiya?" Kulle ido tayi tana murmushi ya lakuce mata hanci tare da manna mata peck a baki sannan ya juya yace "bye" ya tafi. Sauke numfashi Afreen tayi tana lumshe ido dama haka Shuraim ya iya soyayya? Gaskiya idan ya cigaba da nuna mata kalar so haka tasan xata fad'a tarkon son shi, zama tayi taci abincin ta sannan ta tattara kwanukan ta kai kitchen ta wanke Wanda sukayi datti sannan ta wuce d'aki ta bi lafiyar gado don gaskiya bacci take ji.
Comments
Post a Comment